26 Oktoba 2021 - 14:46
​Al-Jabri: Bin Salman Ya Yi Yunkurin Kashe Tsohon Sarkin Saudiyya Abdullah Bin Abdulaziz

Tsohon babban jami’in leken asiri a kasar Saudiyya Saad Al-Jabri ya yi wani tonon silili dangane da wani yunkuri da yariman Saudiyya mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman ya yi, domin kashe tsohon sarkin Saudiyya Marigayi Abdullah Bin Abdulaziz.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wata hira ta tsawon sa’a guda da tashar CBS ta kasar Amurka ta yi da shi, Saad Al-Jabri ya bayyana cewa, Bin Salman mutum ne mai hadari ga daukacin yankin gabas ta tsakiya da ita kanta Amurka da ma duniya.

Ya ce a lokacin da marigayi sarki sarki Abdullah yake kan gadon sarautar kasar, Salman bin Abdulaziz kuma yake a matsayin yarima mai jiran gado, dansa Muhamad Bin Salman ya yi yunkurin kashe sarki, domin mahaifinsa Salman ya karbi sarautar kasar ta Saudiyya.

Tsohon jami’in leken asirin na gwamnatin Saudiyya ya ce, Bin Salman ya bukaci Muhammad Bin Na’if wanda dan amminsa ne, da ya taimaka masa wajen yin amfani da wani zobe da ya samo daga Rasha wanda yake dauke da goba, domin samun damar yin musafaha da sarkin, wanda kuma idan hakan ta wakana, sarkin tashi ta kare, kuma mahaifinsa Salman zai dare kan kujerar sarautar Saudiyya.

Wannan batu dai a lokacin ya nemi jawo wata babbar matsala, amma fadar sarki Abdullah ta warware matsalar ba tare da kowa ya jib a.

Haka nan kuma tsohon jami’in leken asirin ya zargi Bin Salman da yunkurin yi masa kisan gilla kamar yadda ya yi wa Jamal Kashoggi, saboda asiransa da dama da ya sani, amma Allah yana tseratar da shi daga yunkurin kisa.

Duk da cewa gwamnatin saudiyya ta sha bayyana cewa Saad Al-jabri yana fadi karya a kanta, amma shi kuma ya ce dukkanin abin da aka yi an nade shi a bidiyo, kuma dukkanin abin da aka nada yana nan a matsayin hujja.

342/